Facebook Twitter
in Web www.derevoshop.com
An tabbatar da mutane 7,711 sun kamu da cutar Coronavirus
2020-01-30 16:42:38        cri
Hukumomin lafiya a kasar Sin sun sanar a yau Alhamis cewa, mutane 7,711 ne ake da tabbacin sun kamu da cutar numfashi da kwayar cutar Coronavirus ke haifarwa, a larduna 31 na kasar da kuma jihar Xinjiang, ya zuwa jiya Laraba. Inda kuma jimilar mutane 170 suka mutu sanadiyyar cutar.

Hukumar kula da lafiya ta kasar ta fitar cikin rahotonta na kullu yaumin cewa, har yanzu akwai mutane 1,370 dake cikin yanayi mai tsanani, da kuma wasu 12,167 da ake zaton sun kamu da cutar ya zuwa jiya Laraba.

Ta kara da cewa, an kuma sallami mutane 124 daga asibiti, bayan sun samu lafiya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China

 

皇都彩票客户端下载