Facebook Twitter
in Web www.derevoshop.com
An kara samun wadanda suka warke daga cutar numfashi a sassan kasar Sin
2020-01-30 16:17:19        cri
Rahotanni daga asibitocin birane da larduna daban-daban na kasar Sin na cewa, mutanen da a baya suka kamu da cutar numfashin da ta bulla kasar, na kara warkewa daga cutar.

Bayanai na cewa, an sallami marasa lafiya biyu daga asibitin lardin Anhui dake gabashin kasar, da kuma maras lafiya 1 da shi ma aka sallama daga asibitin birnin Chongqing dake yankin kudu maso yammacin kasar.

Marasa lafiyan da aka sallama daga asibitocin masu shekaru 25 da 30 da kuma 44, dukkansu sun yi aiki da kuma zama a Wuhan, birnin da wannan cuta ta bulla. Kuma su ne marasa lafiya na farko da suka warke daga wannan cuta a larduna da ma biranen da suke.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China

 

皇都彩票客户端下载