Facebook Twitter
in Web www.derevoshop.com
Mayakan BH sun kashe masunta 5 a Kamaru
2020-01-30 16:15:20        cri
A jiya Laraba, an gano akalla gawarwakin masunta 5 da mayakan BH suka kashe a yankin arewa mai nisa na Kamaru.

A cewar majiyoyi daga hukumomin tsaro, an farwa ayarin masuntan ne a tsibirin Blangoua dake yankin tafkin Chadi. Masunta na kan hanyarsu ne ta zuwa kamun kifi kamar yadda suka saba, a lokacin da mayakan na BH suka far musu, inda suka kashe tare da raunata wasu.

Kafofin yada labarai na yankin sun ruwaito a jiya cewa, mutane 5 aka kashe.

A cewar rundunar sojin Kamaru, kungiyar BH ta kara tsaurara kai hari kan masunta da manoma a yankin tafkin Chadi a baya bayan nan ne, bisa zarginsu da kwarmata bayanan ayyukanta ga sojoji.

Ko a watan Disamban bara, hukumomi sun ruwaito cewa, kimanin mutane 50 sun mutu sanadiyyar hare-haren BH a yankin Tafkin Chadi, kuma galibinsu masunta ne. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China

 

皇都彩票客户端下载