Facebook Twitter
in Web www.derevoshop.com
WHO ta ce akwai bukatar a yaba tare da girmama kasar Sin bisa kokarinta na yaki da kwayar cutar Coronavirus
2020-01-30 16:10:56        cri
Darakta Janar na hukumar lafiya ta duniya WHO, ya ce kasar Sin ta cancanci al'ummomin kasashen waje su yaba tare da girmama ta, saboda matakai masu tsauri da ta dauka na yaki da barkewar kwayar cutar Coronavirus da kuma hana yaduwarta zuwa kasashen waje.

Da yake jawabi ga manema labarai a Geneva, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya godewa gwamnatin kasar Sin bisa managartan matakan da ta dauka na kare yaduwar kwayar cutar.

Yayin ziyarar Shugaban na WHO, wanda ya koma Geneva daga kasar Sin a jiya Laraba, ya samu ganawa da shugabannin kasar dangane da hada hannu kan aiwatar da matakan dakile cutar a Wuhan da sauran matakan kare jama'a a sauran birane da larduna, da kuma nazarin yadda cutar ke yaduwa da kuma musayar bayanai da sinadarai.

Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya kara da yabawa kasar Sin bisa gano kwayar cutar cikin kankanin lokaci da kuma fitar da bayanai nan take, wanda ya kai ga samar da kayayyakin aikin yaki da cutar cikin gaggawa.

Ya ce hadin gwiwar Sin da Jamus wajen tunkarar barkewar cutar, kyakkyawar alama ce dake nuna yadda Sin ke tuntubar WHO da sauran kasashe bisa goyon baya da hadin gwiwa.

Wani ayarin kwararru na WHO zai ziyarci kasar Sin nan bada dadewa ba, domin kara fahimtar yanayin barkewar cutar da kuma yadda duniya za ta tunkare ta. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China

 

皇都彩票客户端下载