Facebook Twitter
in Web www.derevoshop.com
Gwamnatin Burtnaiya ta baiwa Huawei damar gudanar da aikin samar da fasahar 5G
2020-01-29 21:03:41        cri
Gwamnatin Burtaniya a jiya Talata ta baiwa kamfanin sadarwa na Huawei na kasar Sin takaitaccen iznin samar da fasahar 5G.

Kamfanin Huawei mai hedkwata a birnin Shenzhen wanda ya shahara a fannin samar da na'urorin sadarwa da kayayyakin hidima, ya bayyana cewa, ya samu tabbaci daga gwamnatin Burtaniya cewa, zai ci gaba da hulda da kwastomominsa na ganin aikin samar da fasahar 5G ya kai ga nasara.

Shawarar baya-bayan nan na zuwa ne kimanin shekara guda ke nan, bayan da gwamnatin Burtaniya ta ce, za ta duba ko za ta bar kayayyakin na Huawei su shiga tsarin sadarwar 5G na kasa.

Ana saran sauran kasashen Turai da suka hada da kasar Jamus, su yanke shawarar game da kamfanin na kasar Sin. Shugabannin kasashen Turai sun bayyana cewa, gina fasahar 5G ba tare da kayayyakin Huawei ba, zai kasance mai tsada kuma ba zai kammala a kan lokaci ba,.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China

 

皇都彩票客户端下载