Facebook Twitter
in Web www.derevoshop.com
Kungiyar Taliban ta ce ita ce ta harbo jirgin leken asiri na Amurka
2020-01-28 16:37:23        cri
Kungiyar Taliban a kasar Afghan, ta yi ikirarin harbo wani jirgin leken asiri na Amurka, a ladin Ghazni dake gabashin kasar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar dukkanin mutanen dake cikin jirgin, ciki hadda wani babban jami'in hukumar leken asirin Amurka ta CIA.

To sai dai kuma cikin wani sako da rundunar sojojin Amurka ta fitar a jiya Litinin, ta ce ko da yake akwai tabbacin aukuwar hadarin jirgin, amma ba wasu bayanai da suka tabbatar da cewa Taliban ce ta harbo shi.

Zabiullah Mujahid, wanda ya bayyana kan sa a matsayin kakakin kungiyar ta Taliban, ya wallafa wani sako a shafin sa na Twitter, yana cewa, su ne suka harbo jirgin a yankin Sadokhil, na gundumar Deh Yak, dake lardin Ghazni, da tsakar daren jiya Litinin.

Kafin hakan dai wasu rahotanni sun bayyana cewa, jirgin mallakar kamfanin sufurin jiragen saman Ariana na Afghanistan. Amma daga bisani babban mukaddashin shugaban kamfanin na Ariana Mirwais Mirzakalwal ya yi watsi da rahoton, yana mai cewa jiragen kamfanin na Ariana 2 ne suka yi sufurin fasinjoji a ranar Litinin, kuma dukkanin su sun isa masaukin su lami lafiya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China

 

皇都彩票客户端下载